Kwankwaso Ba Shi Ne Jagoranmu Ba A Jam’iyyar NNPP

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NNPP na Yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Sani Danmasani, ya ce Rabiu Kwankwaso ba jagoran jam’iyyar ba ne, ko a Jihar Kano ko a faɗin ƙasa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Danmasani ya kuma bayyana cewa sauya sheƙar Gwamna Yusuf bai nufin Kwankwaso—wanda tuni aka kore shi daga NNPP—da mambobin tafiyarsa ta Kwankwasiyya sun dawo jam’iyyar ba.

Ya bayyana Gwamna Yusuf a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Jigon NNPP ɗin ya nuna mamaki yadda yawancin kafafen yaɗa labarai a Najeriya ke ci gaba da kiran Kwankwaso a matsayin jagoran NNPP.

A cewarsa, Kwankwaso ya ci amanar jam’iyyar kuma har yanzu yana ƙoƙarin ƙwace ta duk da cewa an kore shi daga cikinta.

Ya ce jam’iyyar na da hujjoji da za su wayar da kan ’yan jarida cewa Kwankwaso, Buba Galadima da wasu sun fice daga jam’iyyar ta hanyar hukuncin ladabtarwa na cikin gida.

“Baya ga matakin ladabtarwa na jam’iyya da ya kai ga korarsu, Kotun Babban Jihar Abia da Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun tabbatar da korar su bisa doka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Kotun Abuja ta fitar da umarnin rajista (enrolment order) da ke hana INEC mu’amala ko gudanar da wani aiki da Kwankwaso da shugabancin NWC na Ajuji, har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

Comments (0)
Add Comment