Kwastam Da NDLEA Sun Kama Tabar Wiwi Ta Naira Biliyan 16.6 Da Aka Yi Fasa Kwaurinta Zuwa Najeriya

Hukumar Kwastam ta Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta NDLEA sun kama wasu manyan kaya na tabar wiwi da aka yi yunkurin shigo da su Najeriya ta haramtacciyar hanya.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Nigeria Customs Service na reshen Tin Can Island Port tare da National Drug Law Enforcement Agency sun kama fakiti 8,347 na Cannabis Indica masu nauyin kilogram 4,173.5.

An kiyasta darajar kayan a kasuwa da kusan Naira biliyan 16.6.

Wannan kamen na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan jami’an hukumomin biyu sun sake kama wasu fakiti 9,450 na tabar wiwi masu nauyin kilogram 4,729 da aka kiyasta darajarsu ta kai Naira biliyan 18.96 a ranar 30 ga watan Afrilu.

Hukumomin sun ce suna ci gaba da ƙara tsaurara matakan tsaro da sa ido domin dakile safarar miyagun ƙwayoyi da ake yi ta tashoshin jiragen ruwa da sauran hanyoyin shiga ƙasar.

Comments (0)
Add Comment