Rahotanni daga karamar hukumar Guri sun ce, wasu maharan makiyaya sun kai hari Yelwan Musari, inda suka kashe wani manoni mai suna Magaji Mai’aya, yayin da wasu suka jikkata wasu mutane ciki har da jami’in ‘yan sanda a rikicin manoma da makiyaya.
Wani shaidar gani da ido, Ado Musa, ya ce makiyayan dauke da makamai sun kai farmaki tsakanin Asabar da Lahadi, sun kone gidaje da injinan nika shinkafa, tare da toshe hanyar Guri zuwa Hadejia, wanda hakan ya hana kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne tun bayan da makiyayan suka kashe wani manomi a bara mai suna Ya’u Namara. An yi yunkurin sasanci tsakanin ɓangarorin biyu, amma bai haifar da mai ido ba tsawon lokaci. Wannan harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani rikici a garin Zarga ta karamar hukumar Taura, inda makiyaya suka jikkata mutum 12.
Har yanzu ba a sami bayani daga jami’an tsaro ba.