Mai Mala Buni ya yi watsi da rahotannin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC zuwa wata kawancen jam’iyyun adawa karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Buni da wasu gwamnoni hudu na APC sun kammala shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP domin kafa kawance gabanin zaben 2027.

Gwamnonin da aka ce suna cikin shirin sauya shekar sun hada da Inuwa Yahaya na Gombe, Nasiru Idris na Kebbi, Hyacinth Alia na Benue, Umaru Bago na Neja, da kuma Mai Mala Buni na Yobe.

Sai dai, a martaninsa, Daraktan Yada Labarai da Huldar Jama’a na Gwamnan, Mamman Muhammad, ya bayyana rahotannin a matsayin kirkirarren labari da kuma zargi maras tushe ko makama.

Ya ce marubutan wadannan sakonni ba su taba kusantar Gwamnan ba, balle su san ko su hango matakin siyasar da zai dauka.

Comments (0)
Add Comment