Majalisar Dattawa Ta Mika Kudurin Yin Takarar Ba Tare Da Jam’iyya Ba

Majalisar dattawa ta umurci magatakardar majalisar da ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirin canza kundin tsarin mulki mai lamba 58 domin ya amince da shi.
Kudirin ya nemi a samar da ‘yan takara masu zaman kansu a zaben shugaban kasa da na gwamna da na majalisun tarayya da na jihohi da na kananan hukumomi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, a cikin wani kudiri da ya gabatar a zaman majalisar na yau, ya ce majalisar dokokin jihar Gombe ta amince da dokokin sauya kundin tsarin mulki masu lambobi 46 da 58 tare da mika matakin nata ga majalisar kasar.
A saboda haka, babban zauren majalisar ya umurci magatakardar da ya mika wa shugaban kasa, kudirin gyara kundin tsarin mulki mai lamba 46.
Kudirin ya nemi sanya shugabannin majalisun kasar cikin mambobin kwamitin tsaro na kasa.

Comments (0)
Add Comment