Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin da zai ayyana garkuwa da mutane (kidnapping) a matsayin aikata ta’addanci, tare da neman a saka hukuncin kisa ga duk wanda aka tabbatar da laifin.
Wannan matsaya ta fito ne bayan zaman majalisar a zaman ranar Laraba 27 ga watan Nuwamba, 2025, inda ‘yan majalisar suka tattauna yawaitar sace-sacen mutane a sassa daban-daban na ƙasar da yadda lamarin ke ƙara ta’azzara duk da matakan tsaro da ake ɗauka.
Sanatoci sun bayyana cewa sace mutane ya zama babbar barazana ga tsaro, tattalin arziki, da walwalar al’umma, lamarin da ya sanya dole a ɗauki matakin doka mai tsauri domin rage yawaitar aikata laifin.
A cewar su, ayyana garkuwa da mutane a matsayin ta’addanci zai baiwa hukumomin tsaro damar samun karin karfi da ikon daukar matakai kai tsaye ba tare da takurawa ta fuskar doka ba.
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta hanzarta bijiro da kudurin sauya dokokin da suka shafi laifuka, domin tabbatar da cewa hukuncin kisa ya zama doka a kan masu garkuwa da mutane, musamman idan an tabbatar da mutuwar wanda aka sace ko kuma an yi amfani da makami.
Wannan matakin na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar yawaitar hare-haren ’yan fashi da masu garkuwa da mutane, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, wanda ya jawo damuwa a tsakanin jama’a da hukumomi.
Majalisar ta jaddada cewa lokaci ya yi da za a dauki tsauraran matakai domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, tare da mayar da hankali wajen ganin an dakile wannan mummunan laifi.