Majalisar Dattawa ta nesanta kanta da umarnin kama Mele Kyari kan binciken Nera tiriliyan 210

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa ba da yawunta aka bayar da umarnin kama tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Nigerian National Petroleum Company Limited, Mele Kyari ba, dangane da binciken zargin batar da kuɗaɗe da ake zargin sun kai Naira tiriliyan 210.

Majalisar ta yi wannan bayanin ne yayin wani zama da kwamitin binciken kuɗaɗen al’umma ke gudanarwa, inda aka samu muhawara kan batun binciken da ke gudana.

Ta ce babu wata takardar hukuma ko amincewa daga Majalisar da ke tabbatar da bayar da umarnin kama Kyari, tana mai jaddada cewa duk wani mataki da za a ɗauka dole ne ya bi ka’idojin doka da tsarin majalisa.

Haka kuma, Majalisar ta yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa bayanan da ba su da tushe, domin kauce wa haifar da ruɗani a cikin al’umma.

A gefe guda, Majalisar ta soki kalaman Sanata Adams Oshiomhole, wanda ya bayyana kamfanin a matsayin “matattarar ɓarayi”, tana mai cewa irin waɗannan kalamai ba su dace da matsayin majalisa ba.

Kwamitin da ke jagorantar binciken ya kuma bayyana cewa kalaman Oshiomhole ba daga cikinsu aka amince da su ba, don haka ba su wakilci matsayar Majalisar ba.

A halin da ake ciki, rahotanni sun bayyana cewa Mele Kyari ya nuna rashin jin daɗi kan umarnin kama shi da aka yaɗa, inda kuma aka ce yana wajen ƙasa domin samun kulawar lafiya.

Majalisar ta tabbatar da cewa binciken zai ci gaba, amma cikin bin doka da ka’idoji na gaskiya da gaskatawa.

Comments (0)
Add Comment