Majalisar Dattijai ta umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo masu garkuwa da mutane da kuma waɗanda ke wallafa bidiyon kuɗaɗen fansa da ake karɓa daga iyalan waɗanda aka sace a shafukan sada zumunta, musamman TikTok.
Majalisar ta bayyana damuwa kan yadda masu laifi ke ci gaba da nuna kuɗaɗen fansa a bidiyo bayan karɓarsu, lamarin da ta ce yana ƙara ƙarfafa aikata laifukan garkuwa da mutane tare da jefa al’umma cikin tsoro.
Sanatoci sun yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki tushen waɗannan bidiyoyi tare da kamo duk masu hannu a yaɗawa ko tallata irin wannan abu, domin dakile yaɗuwar laifukan garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.
Majalisar ta jaddada cewa ya zama dole a ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata irin waɗannan laifuka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma dawo da zaman lafiya a Najeriya.
Ana sa ran hukumomin tsaro za su fara aiwatar da umarnin tare da ƙara sa ido kan kafafen sada zumunta da ake zargin masu laifi na amfani da su wajen yaɗa irin waɗannan bidiyoyi.