Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC), a taronta na 110 da aka gudanar a ranakun 13 da 14 ga Janairu, 2026, ƙarƙashin jagorancin Babban Alƙalin Ƙasa (CJN), Mai Shari’a Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun, ta yanke shawarar miƙa wa Shugaba Tinubu sunayen mutane 14 da suka yi nasara domin naɗa su a matsayin alkalai a Kotun Tarayya (Federal High Court).
Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta NJC, Misis Kemi Babalola-Ogedengbe, ta fitar a daren ranar Alhamis, ta ce a lokacin da majalisar ta gudanar da taron, rahoton tsaro kan ‘yan takarar bai kasance a hannunta ba.
Saboda haka, majalisar ta yanke shawarar jira har sai an gabatar da rahoton tsaron kafin a tura sunayen ‘yan takarar zuwa ga Shugaban Ƙasa.
Bayan samun rahoton tsaron, wanda bai nuna wani abin ƙi ko matsala a kan kowane ɗan takara da aka ba da shawara ba, majalisar a ranar Alhamis, 22 ga Janairu, 2026, ta tura sunayen ‘yan takarar zuwa ga Shugaban Ƙasa.
Mutane 14 da suka yi nasara kuma aka ba da shawarar a naɗa sun haɗa da Babban Magatakardar Kotun Tarayya na yanzu, Suleiman Amida Hassan.
Sauran sunayen su ne Muhammad Barau Saidu, Igboko Chinelo Conchita, Onuegbu Chioma Angela, Galumje Edingah, Ibrahim Vera Eneabo, Abubakar Musa Usman, da Salihu Aisha Yunusa.
Ragowar ‘yan takarar su ne Ikpeme Joy Bassey, Shehu Umaru Adamu, Mohammed Ibrahim Buba, Eigege-Binjin Nendelmum Judith, Usoro Kuyik Uduak, da Nwoye Osinachi Donatus.