Majalisar Wakilai ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan Jihohi

Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi, wanda ke cikin shirin sauye-sauyen kundin tsarin mulkin ƙasa, bayan kada kuri’ar da ta nuna goyon baya mai rinjaye a zauren majalisa.

An gudanar da kada kuri’ar ne a ranar Alhamis a zaman majalisar da Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas, ya jagoranta, inda ‘yan majalisa suka tattauna kan kudirin da aka gabatar ƙarƙashin HB 617.

Bisa sakamakon kada kuri’ar, kusan ‘yan majalisa 289 sun goyi bayan kudirin, yayin da huɗu kawai suka nuna rashin amincewa, abin da ya share fagen ci gaba da matakan sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Kudirin na daga cikin manyan shawarwarin da ke neman sake fasalin tsarin tsaron Najeriya, domin magance matsalolin rashin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, satar mutane da ‘yan bindiga a sassa daban-daban na ƙasar.

A yayin zaman, Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda kuma ke jagorantar Kwamitin Bita na Kundin Tsarin Mulki, ya bayyana cewa wannan sauyi na da nufin rarraba ikon ‘yan sanda zuwa jihohi domin inganta tsaro.

Ya ce tsarin da ake amfani da shi a yanzu, wanda ke karkashin gwamnatin tarayya kawai, ya yi jinkiri wajen kai dauki ga matsalolin tsaro, saboda nisa tsakanin Abuja da wuraren da matsaloli ke faruwa.

A cewarsa, kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen amfani da jami’ai da suka fi sanin yare, muhalli da al’ummar yankunansu, wanda zai inganta saurin daukar mataki.

Majalisar ta kuma bayyana cewa za a ci gaba da nazarin kudirin kafin a tura shi zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa, sannan zuwa Majalisun Jihohi 36 domin samun amincewar akalla kashi biyu bisa uku kafin ya zama doka.

Idan ya kammala matakan amincewa, za a mika shi ga Shugaban Ƙasa domin sa hannu.

A ƙarshe, Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 7 ga Yuli, domin ba ‘yan majalisa damar komawa mazabunsu kafin dawowa ci gaba da nazarin dokokin sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Comments (0)
Add Comment