Majalisar Wakilai ta Tarayya ta fara kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin dokar da ke neman kafa tsarin ’yan sandan jihohi a Najeriya, a wani mataki na gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa.
Ƙudirin dokar na daga cikin muhimman sauye-sauyen da Majalisar Tarayya ke dubawa domin samar da tsarin tsaro da zai bai wa jihohi damar kafa nasu rundunonin ’yan sanda da kuma ƙarfafa aikin tsaron al’umma.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, wanda ke jagorantar kwamitin duba kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa ƙudirin ya zama dole duba da ƙaruwar matsalolin tsaro kamar ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ’yan bindiga a sassan ƙasar nan.
Masu goyon bayan ƙudirin na ganin cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma saurin magance matsalolin da suka shafi yankuna daban-daban, yayin da masu adawa ke nuna fargabar yiwuwar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taba bayyana goyon bayansa ga wannan ƙudiri, yana mai cewa zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.
Ana sa ran dukkan mambobi 360 na Majalisar Wakilai za su shiga kaɗa ƙuri’ar da za ta tantance makomar wannan muhimmin ƙudiri.