Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana damuwa kan karuwar tarin basukan da Najeriya ke karbowa wanda yace ya wuce gona da iri a doka, yana mai cewa hakan na zama barazana ga dorewar tattalin arziƙin kasa.
Yayin taron ƙungiyar kwamitocin lissafin kuɗi na kasashen yammacin Afirka a Abuja, Tajuddin ya jaddada bukatar tsauraran matakan bincike, da kuma tabbatar da cewa duk bashin da aka karbo ya amfani al’umma kai tsaye.
Tajuddin ya ce Najeriya za ta jagoranci kafa sabon tsarin lura da bashin kasashen yammacin Afirka wanda zai daidaita rahotannin bashi, ya fayyace tsarin gaskiya, tare da bai wa majalisu bayanan lokaci don su kula da hanyoyin lamuni.
Ya gargadi cewa cin bashi domin cike gibin ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi da masana’antun samar da ayyukan yi ya dace, amma a kauce wa bashi marar amfani wanda ke ciyar da rashawa ko amfani na siyasa.