Majalisar Zartarwa ta Jigawa ta amince da manyan ayyukan ci gaban lafiyar jihar

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta gudanar da zamanta na farko a ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi, inda ta amince da muhimman shawarwari da suka shafi fannonin lafiya, makamashi, muhalli da ci gaban gwamnati.

A cikin taron, majalisar ta amince da shirin Jihar na shiga cikin Green Nigeria Challenge – Jigawa State Edition, wani shiri da ke da nufin inganta muhalli, rage hamada, da ƙara yawan bishiyoyi a faɗin jihar.

Gwamnatin ta ce shirin zai taimaka wajen yaƙi da sauyin yanayi, dawo da ƙasar da ta lalace, da kuma ƙarfafa al’umma wajen kula da muhalli. Haka kuma, an umarci Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi da ta haɗa kai da al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu domin tabbatar da nasarar shirin.

Majalisar ta kuma amince da ƙarin ayyuka a kan ginin cibiyar samar da iskar oxygen ta cryogenic da ke Dutse, domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya a jihar.

An ware kimanin Naira biliyan 1.22 domin wannan ƙarin aiki, wanda ya sa jimillar kuɗin aikin ya kai Naira biliyan 3.42.

Haka kuma, majalisar ta amince da rabon Naira miliyan 362.8 a ƙarƙashin asusun BHCPF, wanda za a raba wa cibiyoyin lafiya na matakin farko (PHC) guda 281 a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Majalisar ta kuma amince da sake duba farashi da faɗaɗa aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana (Solar Mini-Grid) a manyan cibiyoyin gwamnati, ciki har da Gidan Sakatariya, Ma’aikatar Shari’a, da Majalisar Dokoki ta Jiha.

An ƙara kuɗin aikin daga Naira biliyan 6.08 zuwa Naira biliyan 7.46, tare da faɗaɗa ƙarfin tsarin zuwa 3MWp da batir mai ƙarfin 4.5MWh.

Comments (0)
Add Comment