Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar yunwa da talauci, da kuma hada kan shirye-shiryen rage fatara da ake ci gaba da aiwatarwa a fadin kasa.
Wannan matsaya ta biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da ‘yar majalisar Yobe, Khadija Ibrahim, ta gabatar a zaman majalisar da aka yi a wannan Alhamis din.
Rahotanni sun nuna cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 139, wato kashi 61 cikin 100, na rayuwa a karkashin layin talauci, kuma ana hasashen adadin zai kai miliyan 141 nan da shekarar 2026 sakamakon hauhawar farashi da raunin tattalin arziki.
Kasar na kuma fuskantar babbar barazanar rashin wadataccen abinci, inda Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kusan ‘yan Najeriya miliyan 35 za su fuskanci matsanancin karancin abinci a 2026, mafi yawa a nahiyar Afirka.
Khadija ta bayyana cewa miliyoyin ‘yan kasa ba sa iya sayen abinci da muhimman bukatu, lamarin da ke kara tsananta yunwa da rashin gina jiki, musamman ga mata, yara, tsofaffi da ‘yan gudun hijira, tare da jaddada cewa yankin Arewa maso Gabas ne ya fi fama da matsalar.
Bayan amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta karfafa da kuma hada kan shirye-shiryen rage talauci da tsaron abinci, tare da umartar ma’aikatun da abin ya shafa su tallafa wa manoma a yankunan da rikici ya shafa domin farfado da noma da bunkasa samar da abinci.