Makinde Ya Zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APM a Zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) a babban zaɓen shekarar 2027, bayan kammala tsarin zaɓen cikin gida na jam’iyyar.

Makinde ya karɓi takardar shaidar tsayawa takara (Certificate of Return) a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, inda ya bayyana cewa zai mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki, inganta shugabanci da samar da mafita ga matsalolin da ke addabar Najeriya.

Tun da farko, Makinde ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin ƙasa a wani gangamin siyasa da aka gudanar a Ibadan, tare da bayyana haɗin gwiwa tsakanin wasu tsagin PDP da APM domin tunkarar zaɓen 2027.

Shugaban jam’iyyar APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ya bayyana fitowar Makinde a matsayin wani muhimmin mataki ga jam’iyyar, yana mai cewa hakan zai ƙara wa APM ƙarfi a siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.

Sai dai matakin ya janyo martani daga wasu ‘yan siyasa, inda aka samu muhawara kan batun haɗin gwiwar PDP da APM da kuma tasirin da hakan zai yi a zaɓen mai zuwa.

Comments (0)
Add Comment