Wani malamin makaranta a Hadejia ya yi kira ga iyaye da su rika tura ‘ya’yansu makaranta da wuri domin su amfana da darussan da ake koyarwa tun da safe.
Malamin, wanda ke koyar da darasin Turanci (English), ya bayyana cewa duk da lokacin fara karatu da ƙarfe 8:00 na safe, sau da yawa ɗalibai kaɗan ne kawai ke zuwa a lokacin.
A cewarsa, yana cikin makaranta karfe 7:30 na safe, amma dalibai biyu ne kadai a harabar makarantar.
Ya ce wasu ɗaliban kan ci gaba da shigowa makaranta har zuwa kusan ƙarfe 9:00 na safe, lamarin da ke sa su rasa darussan farko da ake koyarwa.
A cewarsa, mafi yawan lokutan koyar da darasin Turanci suna kasancewa ne a farkon jadawalin karatu, wanda hakan ke nufin ɗaliban da suka makara ba sa samun damar amfana da darussan.
Saboda haka, ya roƙi iyaye da su ƙara sa ido tare da tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna zuwa makaranta a kan lokaci domin samun cikakkiyar ilimi.