Malami ya musanta zargin gano makamai a gidajen da ake dangantawa da shi

Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke ikirarin cewa an gano makamai a wasu gidaje da ake zargin nasa ne.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mohammed Bello Doka, ya fitar, Malami ya ce babu wata hukuma ta tsaro da ta sanar da shi, iyalansa ko lauyoyinsa game da gano makamai a ko ina da ake dangantawa da shi. Ya kuma nesanta kansa daga duk wata alaƙa da ta’addanci ko daukar nauyin ta’addanci, yana mai cewa zarge-zargen ba su da hujja ko sahihiyar shaida.

Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan yadda aka hana Malami ganawa da iyalansa da lauyoyinsa tun bayan kama shi, lamarin da ya ce ya saɓa wa dokokin ƙasa. Malami ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su bi ƙa’idojin aikin jarida, su bambanta tsakanin zargi da gaskiya, tare da barin doka ta yi aikinta ba tare da tsangwama ba.

Comments (0)
Add Comment