Masarautar Hadejia Ta Fitar Da Jadawalin Bukukuwan Babbar Sallah Na Bana

Majalisar Masarautar Hadejia ta sanar da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Babbar Sallah ta bana, tare da bayyana ranakun hawa.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Abubakar Suleiman, ya sanya wa hannu, an ce za a gudanar da sallar Idi a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 8:00 na safe a filin Idi na Mai Martaba.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da hawan bariki a ranar Alhamis 28 ga watan Mayu da ƙarfe 8:00 na safe, yayin da hawan ziyara zai gudana ranar Juma’a 29 ga watan Mayu da ƙarfe 4:00 na yamma.

Haka kuma, majalisar ta bayyana cewa za a fara shigowa Hadejia da dawakai domin bukukuwan tun daga ranar Litinin 25 ga watan Mayu, tare da buƙatar masu unguwanni da makada su shiga ranar Talata 26 ga watan Mayu domin gudanar da bukukuwan cikin tsari da walwala.

Comments (0)
Add Comment