Dalibi a Jami’ar Bayero Kano (BUK), Umar Abdullahi Hafizi, ya rasu bayan masu kwacen waya sun kai masa hari a gidansu dake Dorayi, Gwale LGA, Kano, inda suka daba masa wuƙa suka kwace wayarsa.
Lamarin ya faru ne da ƙarfe 11 na daren Lahadi. An cafke mutane huɗu da ake zargi tare da makamai. An yi jana’izar sa a Zaria, Kaduna. Jami’ar BUK ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, tare da kira ga ɗalibai su ƙara kula da tsaronsu.
Umar ɗalibi ne a matakin shekara ta uku a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), a sashen Zaman Takewa da Ilimin Sanin Laifuka (Sociology and Criminology).