Masu Sukar Tinubu Za Su Kunyata A Zaɓen 2027 — Matawalle

Ƙaramin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ce masu sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su kunyata saboda irin nasarorin da gwamnatinsa ke samu da za su tabbatar masa da nasara a Zaɓen 2027.

Matawalle ya bayyana masu sukar shugaban a matsayin masu yaɗa ƙarya da farfaganda, yana mai cewa hakan ba zai hana Tinubu ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban ƙasa ba.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da fifiko a harkar tsaro, tattalin arziki, ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma, a yayin da take ƙara tallafa wa jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar nan.

Ministan ya yi kira ga matasa da su guji yaɗa bayanan ƙarya, su rungumi abubuwan da za su kawo ci gaba da haɗin kai a ƙasa.

Matawalle ya yi waɗannan kalamai ne a wani taron wayar da kai da aka shirya a Sakkwato domin ƙarfafa goyon baya ga Shugaba Tinubu gabanin Zaɓen 2027.

Comments (0)
Add Comment