MATASA BIYU SUN RASA RAYUKANSU A CIKIN WANI DAM YAYIN DA SUKE KOKARIN TSEREWA DAGA SAMAMEN HUKUMAR NDLEA, A KARAMAR HUKUMAR KAZAURE A NAN JIHAR JIGAWA.

Wasu matasa biyu sun rasa rayukansu bayan nutsewa a cikin wani dam yayin da suke kokarin tserewa daga samamen hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, a karamar hukumar Kazaure a nan Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar lokacin da jami’an hukumar suka kai farmaki kan wani wurin da ake zargin ana harkar kwaya a unguwar Ganguli, inda hakan ya sanya wasu matasa da dama suka ranta ana kare.

Wadanda suka mutu an bayyana su da Garzali Garba mai shekaru 22 daga unguwar Tsohon Kafib  da kuma Usama Ahmed mai shekara 21 daga unguwar Kanti, dukkansu daga Kazaure, inda suka yi yunƙurin tserewa ta hanyar nutsewa cikin dam amma suka gamu da ajalinsu.

Haka kuma an ƙara tsaro a ofishin NDLEA na Kazaure, tare da tattaunawa da shugabannin al’umma domin kwantar da hankali da tabbatar da zaman lafiya a garin.

Comments (0)
Add Comment