Mayaƙan Boko Haram sun fille kan wasu mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke Jihar Borno

Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun kashe mata biyu ta hanyar fille musu kai a yankin Dutsen Mandara, Gwoza, Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce an yi wa matan kisan ne bisa zargin yin sihiri (shirka), bayan an same su da layu a lokacin bincike.

Mayaƙan sun ɗauki matan zuwa tsaunuka suka aiwatar da hukuncin a bainar jama’a domin tsoratar da al’umma da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar.

Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsananta hukunci a watannin baya, musamman kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri, ko yunkurin tserewa daga yankin da suke iko.

Comments (0)
Add Comment