Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar Ya Ajiye Aikinsa

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ajiye aikinsa na minista ranar Litinin.

A wata takardar ajiye aiki da ya miƙa ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Tuggar ya bayyana godiyarsa ga shugaba Bola Tinubu da ya ba shi dama.

Duk da dai ambasada Tuggar bai faɗi dalilin ajiye aikin ba, amma bayanai na nuna ya ajiye aikin ne domin tsaya takarar gwamna a jihar Bauchi.

Tuggar shi ne minista a gwamnati shugaba Tinubu da ya fara ajiye aikinsa domin tsayawa takara kafin cikar wa’adin da shugaba Tinubu ya ba su na ajiye mukamin gwamnati.

Comments (0)
Add Comment