Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu nasarar da ta kai kashi 65 zuwa 70 cikin ɗari a fannin tsaro, inda ya ce an samu raguwar ta’addanci a ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da ARISE News, inda ya ce duk da ƙalubale da ake fuskanta, musamman satar ɗalibai a makarantu, an samu gagarumin ci gaba wajen rage ayyukan ‘yan ta’adda a wasu yankuna.
Musa ya ce matsalar tsaro a Najeriya ba za a dora ta kacokan kan gwamnati ba, yana mai cewa lalacewar tsarin iyali da zamantakewa na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da laifuka kamar sace-sacen mutane.
Ya kuma jaddada cewa sojojin Najeriya na samun gagarumin haɗin kai daga jama’a da abokan hulɗa na ƙasashen waje, wanda ya taimaka wajen inganta ayyukan yaki da ta’addanci.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa a baya-bayan nan an samu ƙaruwa a hare-haren satar ɗalibai, musamman a jihohin Borno da Oyo, inda aka sace ɗalibai da dama tare da asarar rayuka a wasu hare-hare.
Ministan ya ce gwamnatin na aiki tare da ƙasashe kamar Amurka, Birtaniya, Faransa, Brazil da Turkiyya domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a Najeriya.