Tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi makudan kuɗaɗe daga gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A cewar Muhuyi Magaji, a watan Disamban 2023 an bai wa Kwankwaso Naira biliyan 1 da dubu 50,000 domin gina gida. Ya kuma yi zargin cewa an sake ba shi Naira miliyan 525 domin gina ofis, sannan daga bisani aka ba shi Naira biliyan 1 da miliyan 240 da dubu 400 domin sayen motoci guda biyu.
Haka kuma, ya ce a watan Yunin 2024, an ba Kwankwaso Naira miliyan 100 da dubu 80 a matsayin kuɗin magani, tare da Naira miliyan 510,213,000 domin tafiyar hutu.
Muhuyi Magaji ya ce waɗannan bayanai na cikin takardun baitul malin Jihar Kano, yana mai ƙalubalantar Kwankwaso da ya kai shi kotu idan har ya yi ƙarya.
Sai dai, har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga Rabiu Musa Kwankwaso ko gwamnatin Jihar Kano da ta tabbatar ko ta musanta waɗannan zarge-zarge.