Muna Yaƙi da Barazanar Tsaro da Neman Haɗin Kan Al’umma — NSCDC

Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Gombe ta yi kira ga al’umma, shugabannin gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro.

Hukumar ta ce hakan zai inganta tattara bayanan sirri da kuma daƙile sabbin barazanar tsaro da ke tasowa a faɗin jihar.

Kiran ya fito ne daga bakin Kwamandan NSCDC na Jihar Gombe, Jibrin Idris a yayin taron tattaunawa kan harkokin tsaro da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis a Gombe.

Idris ya bayyana cewa, taron a matsayin wani muhimmin mataki na gina tsarin tsaro mai ɗorewa ta hanyar haɗin gwiwa, amincewa da juna da kuma ɗaukar nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare.

Ya ce, babu wata gwamnati ko hukuma ɗaya tilo da za ta iya tabbatar da cikakken tsaro ba tare da goyon bayan al’umma ba, yana mai jaddada cewa jama’a su ne tushen sahihan bayanan sirri da ke taimakawa wajen hana aikata laifuka kafin su faru.

“Nasarar harkokin tsaro tana ta’allaka ne kan yadda jama’a da hukumomin tsaro ke musayar bayanai cikin lokaci tare da gina amincewa da juna,” in ji shi.

Kwamandan ya buƙaci mazauna jihar da su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallansu tare da kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga hukumomin da abin ya shafa.

Ya kuma jaddada muhimmancin kare muhimman kadarorin gwamnati da suka haɗa: da cibiyoyin samar da wutar lantarki, kayayyakin sadarwa, makarantu, gadoji da hanyoyin samar da ruwa, yana mai cewa lalata waɗannan kadarori na da illa ga ci gaban al’umma.

Idris ya tabbatar wa mahalarta taron cewa, duk bayanan sirri da aka miƙa wa NSCDC za a kiyaye su cikin sirri tare da ɗaukar matakan da suka dace cikin ƙwarewa da gaskiya.

Ya kuma sha alwashin cewa, hukumar ba za ta bari masu aikata laifuka su samu mafaka a ko’ina cikin jihar ba.

Kwamandan ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin sa-kai bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.Kwamandan NSCDC na Jihar Gombe, Jibrin Idris,

Comments (0)
Add Comment