Mutane 19 ne akalla aka tabbatar da mutuwarsu a Kano

Akalla mutane 19 ne aka tabbatar da mutuwarsu a karamar hukumar Doguwa da ke jihar Kano bayan da ambaliyar ruwa tayi awon gaba da wata mota da suke tafiya a ciki.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a bayan wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin.

HakiminDoguwa, Alhaji Yusif Umar Doguwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ya zuwa yanzu, an gano gawawwaki 15 yayin da aka tsananta bincike don gano sauran mutane 4 da iftila’in ya rutsa da su.

Umar Doguwa ya ce ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da motar ne bayan injin ta ya mutu a tsakiyar wata gada da suke kokarin tsallakawa.

Ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta mamaye gadar sakamakon ruwan sama da aka tafka a daren Juma’a.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar, Ali Abdullahi Garko shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Comments (0)
Add Comment