Mutane Dubu 21 Na Rayuwa da Cutar HIV/AIDS a Jihar Jigawa

Hukumar Yaki da Cutar HIV/AIDS ta Jihar Jigawa (JISACA) ta bayyana cewa jihar na daga cikin jihohin Najeriya da ke da mafi ƙanƙantar adadin masu dauke da cutar, duk da kalubalen da ake fuskanta a yaki da cutar.

Manajan hukumar, Ibrahim Almajiri, ya bayyana haka a shirin “Jigawa A Yau” na Radio Jigawa, yayin bikin Ranar Yaki da Cutar HIV ta Duniya na bana. A cewarsa, kimanin mutane dubu 21 ke rayuwa da cutar a fadin jihar — adadi mai ƙasa idan aka kwatanta da wasu jihohin kasar.

Ya ƙara da cewa mutane dubu 16 daga cikin adadin sun riga sun shiga shirin karɓar maganin antiretroviral, wanda ya taimaka wajen rage yaduwar cutar da kuma inganta lafiyar masu dauke da ita.

Duk da cewa kungiyoyin duniya da dama sun janye tallafi, gwamnati ta kaddamar da shirin maye-gurbi domin tabbatar da cewa masu dauke da cutar ba su fuskantar tsaiko wajen magani da tallafi.

JISACA ta tabbatar da cewa jihar na da cikakkiyar damammaki wajen cimma burin kawo ƙarshen cutar nan da 2030, bisa tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Comments (0)
Add Comment