Mutum 12 sun Jikkata a Sabon Rikicin Manoma da Makiyaya A Taura, Jihar Jigawa

Akalla mutane 12 sun jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya barke a ƙauyen Zarga, karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa, sakamakon zargin kutse a gonakin mutanen yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Taura, Shuaibu Hambal, ya ce rikicin ya fara ne bayan makiyaya sun shiga gonar wani matashi manomi, suka kuma harbe shi da kibau lokacin da ya yi ƙoƙarin hana su.

Mutanen ƙauyen Zarga suka tattaru domin ceto wanda ya jikkata, lamarin da ya rikide zuwa tarzoma inda makiyayan suka sake afkawa jama’ar garin da kibau, har ta kai ga sun jikkata mutane 12.

A halin yanzu, an kwantar da wadanda suka jikkata a asibitoci daban-daban domin duba lafiyarsu.

Rundunar ‘yan sanda ta isa wurin, ta kuma kama mutum ɗaya daga ɓangaren makiyayan.

Wannan ya biyo bayan irin wannan rikici da ya faru kwanaki kaɗan da suka gabata a Birnin Kudu, inda mutane 6 suka jikkata.

Rahoton ya nuna cewa rikice-rikicen manoma da makiyaya a Jigawa na da dangantaka da raguwar wuraren kiwo, yawan ƙaura da makiyayan ke yi daga wasu sassan kasar nan har da ma ketare, da kuma tasirin dumamar yanayi, wanda ke tilasta makiyaya shiga yankunan noma a neman ruwa da ciyawa da za su ciyar da dabobinsu.

Comments (0)
Add Comment