Naira ta samu Gagarumar Daraja A Kan Dalar Amurka A Dukkan Kasuwannin Canjin Kuɗi

Naira ta samu gagarumin daraja a kan dalar Amurka a kasuwannin canjin kuɗi na hukuma da na kasuwar bayan fage (black market), inda ta rufe makon cikin kyakkyawan yanayi.

Bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa a ranar Juma’a Naira ta ƙara ƙarfi zuwa N1,386.55 kan kowace dala, daga N1,396.99 da aka canja a ranar Alhamis.

Wannan na nufin cewa a rana guda, Naira ta ƙarfafa da N10.44 a kan dalar Amurka.

Haka kuma, a kasuwar bayan fage (black market), Naira ta samu ƙarin N10 inda ta rufe a kan N1,470 a ranar Juma’a, daga N1,480 a ranar da ta gabata.

Bincike ya nuna cewa a ma’aunin mako zuwa mako (week-on-week), Naira ta samu ƙarin N35.08 a kasuwar hukuma da kuma N20 a kasuwar bayan fage.

Ci gaban da Naira ke samu a dukkan kasuwannin canjin kuɗi ya zo ne yayin da ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar (foreign reserves) ya ƙaru zuwa dala biliyan $46.18 a ranar 29 ga Janairu, 2026, daga dala biliyan $46.01 da aka samu a Juma’ar makon da ya gabata.

Comments (0)
Add Comment