Rukunin ƴan Najeriya na biyu sun dawo gida daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan da aka samu jinkiri a shirin na kwashe mutane sakamakon tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙin jinin ƴan ci-rani.
Fiye da ƴan Najeriya 260 ne suka isa Legas a ranar 11 ga watan Yuni bayan da suka yi rajistar dawowa da radin kansu sakamakon ƙaruwar ƙyamar baƙi da kuma fargabar tashin hankali a sassan Afirka ta Kudu.
A ranar 15 ga watan Yuni ne dai aka sa ran tashin jirgin na biyu, sai dai an samu jinkirin gudanar da aikin, lamarin da ya sa ƴan Najeriya da dama da shirin ya shafa shiga halin rashin tabbacin lokacin da za su iya tashi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Kimiebi Ebienfa, ya shaida wa BBC a ranar Alhamis cewa “‘wasu ƴan Najeriya ” sun koma gida da sanyin safiyar yau.
Ya ce an dawo da “kusan mutane 50” daga Afirka ta Kudu, ya kuma ƙara da cewa ƴan Najeriya 700 da suka yi rajistar shirin ƙwashe mutanen na nan suna jiran ranar dawowar su.
Sama da ƴan Najeriya 1,000 ne suka fara nuna sha’awar komawa gida bayan zanga-zangar ƙin jinin baƙi da kuma hare-haren da ake kai wa ƴan ƙasashen ƙetare ya bazu zuwa wasu sassan ƙasar Afirka ta Kudu, a cewar jami’an Najeriya.