Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya na shan fiye da lita biliyan 2.5 na ruwan leda (sachet water) a duk shekara, wanda fiye da masana’antu 32,000 ke samarwa a fadin kasar nan.
Darakta Janar na Hukumar Kare Muhalli ta Kasa (NESREA), Farfesa Innocent Barikor, ne ya bayyana hakan a yayin taron fara aiwatar da shirin GEF Child Project 11193 a birnin Abuja.
Ya ce shirin na da nufin rage yawan amfani da ruwan leda tare da tabbatar da samun ruwan sha mai tsafta ga al’umma. A cewarsa, duk da sauƙin da ruwan leda ke kawo wa jama’a, ya haifar da mummunar illa ga muhalli, ciki har da toshe magudanan ruwa, ambaliya, lalata halittu da barazana ga lafiyar jama’a.
Barikor ya ce matsalar samun ruwan sha da gurbacewar muhalli sakamakon robobi na sa shirin ya zama mai matuƙar muhimmanci a wannan lokaci.
Ya ƙara da cewa shirin GEF 11193 wani muhimmin tsari ne da ya dace da manufofin kare muhalli na Najeriya, inda zai mayar da hankali kan kariya, kirkire-kirkire, sauye-sauyen manufofi da ingantaccen tsarin kula da shara.
A sakon fatan alheri, wakiliyar UNEP, Isabella Vanderbeck, ta ce Najeriya muhimmiyar abokiya ce wajen yaƙi da gurbacewar muhalli da robobi. Ta yi kira da a rage amfani da robobi domin kare muhalli.
Haka zalika, wakiliyar GEF, Evelyn Swain, ta tabbatar da kudurin kungiyar na ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen rage amfani da ruwan leda guda ɗaya tare da samar da ruwan sha mai aminci.
A nata bangaren, Zuliat Mohammed, Babbar Jami’ar Kimiyya a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabta ta Tarayya, ta bayyana shirye-shiryen ma’aikatar na haɗin gwiwa da NESREA domin nasarar shirin.