Najeriya ta sake buɗe iyakokinta da ƙasashen Benin da Jamhuriyar Nijar a Jihar Kebbi, domin ƙarfafa kasuwanci tsakanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da juna. Hukumar Kwastam ta Ƙasa reshen Jihar Kebbi ce ta sanar da buɗe iyakokin Kamba da Tsamiya.
Iyakokin dai suna cikin ƙananan hukumomin Dandi da Bagudo, kuma an ce an buɗe su ne domin sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyakin kasuwanci tsakanin Najeriya, Benin da Nijar.
Tun da farko, an rufe iyakokin ne sakamakon ƙara ta’azzarar matsalolin tsaro a yankunan kan iyaka, lamarin da ya kawo cikas ga kasuwanci da zirga-zirgar jama’a.
Sai dai bayan jerin tattaunawa da cimma matsaya tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin, aka yanke shawarar sake buɗe iyakokin domin dawo da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.
Yayin buɗe iyakokin a ranar Litinin, Kwamandan Kwastam na Jihar Kebbi, Mahmud Matawalle Ibrahim, ya ce an ɗauki matakin ne bisa amincewar Shugaban Ƙasa, domin ba da damar motsa halal ɗin kayayyaki daga iyakar Tsamiya zuwa Jamhuriyar Nijar ta hanyar iyakar Kamba.
Ya bayyana cewa matakin ya ba da damar share manyan motoci da dama da suka makale daga Jamhuriyar Benin, inda aka bari su wuce zuwa iyakar Tunga Jado ta Nijar ta cikin Kebbi.
Hukumar Kwastam ta ce buɗe iyakokin zai ƙara bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen uku, tare da ƙarfafa tsaro, ganin yadda kowanne ɓangare ya yi alƙawarin bin yarjejeniyar da aka cimma domin tabbatar da cewa an gudanar da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.