Najeriya Ta Zama Ta Uku A Duniya Wajen Cin Bashin Bankin Duniya Da Dala Biliyan 18.5

Najeriya ta zama ƙasa ta uku a duniya wajen yawan bashin da ake bin ta daga Bankin Duniya, inda adadin bashin ya kai Dala biliyan 18.5.

Majiyoyi sun haɗa da rahoton Bankin Duniya kan bashin ƙasashe masu tasowa da kuma bayanan ma’aikatar kuɗi ta Najeriya kan rancen ƙasashen waje.

Masana tattalin arziki na bayyana cewa yawan bashin na iya ƙara taimakawa wajen aiwatar da manyan ayyuka idan aka yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata, sai dai sun gargadi gwamnati da ta tabbatar da kula da yadda ake kashe kuɗaɗen domin kauce wa ƙara nauyin bashi a nan gaba.

A baya-bayan nan gwamnatin tarayya ta ce tana amfani da rancen wajen tallafa wa fannoni kamar samar da wutar lantarki, gine-ginen ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da kuma rage talauci.

Sai dai wasu masana da ƴan adawa sun nuna damuwa kan yadda bashin ƙasar ke ƙaruwa, suna masu cewa hakan na iya haifar da ƙarin matsin tattalin arziki idan ba a samu hanyoyin bunƙasa kuɗaɗen shiga ba.

Comments (0)
Add Comment