Natasha ta bawa Sanata Akpabio hakuri cikin wasika mai cike da zolaya

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar majalisar da aka dakatar daga wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta rubuta wata wasika inda ta bayar da wani irin uzuri ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan zargin cin zarafi da ta yi masa a baya.

Sai dai wasikar nata na dauke da salon zolaya, kuma ta rubuta ta ne a lokacin da Akpabio ke Rome domin halartar jana’izar marigayi Paparoma Francis.

Idan dai za’a iya tunawa Sawaba Radio ta ruwaito yadda, aka dakatar da Sanata Natasha a ranar 6 ga Maris, bayan sabani mai zafi da shugabancin majalisar, kan sabon tsarin zama da aka gabatar wanda ta ce an tsara shi ne don tauye mata hakkinta.

Lamarin ya kazanta ne bayan da ta bayyana a talabijin inda ta zargi Akpabio da yin ramuwar gayya bayan ta ki amincewa da bukatar sa ta neman lalata da ita.

A yayin taron wani Mata da aka gudanar a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Natasha ta bukaci a shiga tsakani domin duba yadda ake tafiyar da al’amura a majalisar dattawan Najeriya.

Haka kuma, ta koka kan yadda aka dauki matakai masu tsauri a kanta, ciki har da janye mata jami’an tsaro, dakatar da albashinta, da kuma dakatar da ita daga majalisar har na tsawon watanni shida.

Comments (0)
Add Comment