NCDC ta ce kimanin mutane 637 ne suka harbu da cutar Corona a jihohi 18

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane 637 ne suka harbu da cutar Corona a jihohi 18 da suke Najeriya ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton na NCDC Kamar Kullum jihar Lagos ce a kan gaba da mutane 322 da suka harbu da cutar sai Rivers 70 Edo 54.

Sauran Jihohin sune Delta (34), Akwa Ibom (31), Kwara (31), FCT (29), Ekiti (17), Ogun (14), Osun (10), Kebbi (8), Cross River (5), Plateau (3), Taraba (3), Kaduna (2), Bayelsa (2), Benue (1), Enugu (1) and Kano (1).

NCDC ta ce an sammali Marasa Lafiya 347 da suka warke daga cutar, inda kuma aka samu mutane 7 da cutar ta hallaka a jiya.

Kawo yanzu kimanin Mutane dubu 188,880 ne suka harbu da cutar tun bayan bayyanarta a Najeriya haka kuma an sallami mutane dubu 169,382 da suka warke daga cutar, yayin da kuma ta hallaka mutane dubu 2,288 a Najeriya.

Comments (0)
Add Comment