Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takararta a Jihar Kano domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin jerin da jam’iyyar ta wallafa, ta ayyana Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a Kano, yayin da aka kuma bayyana sunayen ‘yan takarar kujerun Sanata guda uku na jihar.
A kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, jam’iyyar ta zaɓi Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, yayin da Engr. Sunusi Usman Dambatta zai fafata a Kano ta Arewa. Haka kuma, Kasim Ibrahim Bataiya ne aka tsayar takara domin wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa.
NDC ta kuma bayyana sunayen ‘yan takararta na Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabu 24 na jihar, ciki har da tsoffin jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa. Daga cikin su akwai AVM Ibrahim Umar (mai ritaya) a Dala, DCP Aminu Ado Aliyu (mai ritaya) a Ghari/Tsanyawa da kuma Prof. Salisu Muhammad Tudun Wada a Karaye/Rogo.
Hakazalika, jam’iyyar ta fitar da sunayen ‘yan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazabu 40, inda ta tsayar da ‘yan takara a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa matakin zaɓen ‘yan takarar ya biyo bayan tuntuba da shawarwari da shugabanni da masu ruwa da tsaki suka gudanar domin tabbatar da haɗin kai da ƙarfafa jam’iyyar kafin zaɓen 2027.