Jam’iyyar National Democratic Coalition (NDC) ta bayyana cewa ba za ta tilasta wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sanya hannu kan rantsuwar kin sauya sheka da ta ƙaddamar ba.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Ikenna Enekweizu, ya bayyana cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin NDC ya tanadi cewa duk masu neman takara su sanya hannu kan wannan rantsuwa, shugabannin jam’iyyar sun yanke shawarar keɓe Obi da Kwankwaso daga wannan sharadi.
A cewarsa, manufar rantsuwar ita ce dakile yawaitar sauya shekar da ’yan majalisun tarayya da na jihohi ke yi bayan sun samu nasara a zaɓe, domin kare martaba da haɗin kan jam’iyyar.
Enekweizu ya ce matakin bai shafi shugaban ƙasa ko gwamnoni ba, domin an fi mayar da hankali kan ’yan majalisun da ake zaɓa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar, da nufin hana su sauya sheka bayan sun samu muƙami.
Ya ƙara da cewa NDC na da burin gina jam’iyya mai ɗorewa wadda ke da biyayya da tsari mai ƙarfi, yana mai jaddada cewa keɓe Obi da Kwankwaso daga rantsuwar ba yana nufin suna da niyyar sauya sheka ba ne, sai dai wani mataki ne na shugabanci da jam’iyyar ta ɗauka.