NDC Ta Tabbatar da Peter Obi da Kwankwaso a Matsayin Tikitin Shugaban Ƙasa na 2027

Jam’iyyar NDC ta tabbatar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, tare da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A cewar jam’iyyar, an amince da tikitin ne bayan kammala shawarwari da tuntuba tsakanin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, inda aka bayyana cewa haɗin gwiwar jagororin biyu zai taimaka wajen ƙarfafa matsayin jam’iyyar a babban zaɓen da ke tafe.

Shugabannin NDC sun bayyana cewa zaɓin Obi da Kwankwaso ya samo asali ne daga ƙwarewarsu a harkokin mulki, shugabanci da kuma irin goyon bayan da suke da shi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su haɗa kai domin ganin an samu nasara a zaɓen 2027, tana mai jaddada aniyarta ta samar da shugabanci nagari da ci gaban ƙasa.

Comments (0)
Add Comment