Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta bankado sabbin dabarun da masu fataucin kwayoyi ke amfani da su wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi cikin kayayyakin yau da kullum.
Hukumar ta ce an gano yadda ake ɓoye ƙwayar methamphetamine a cikin yoghurt da kuma na’urorin MP3, domin shigar da su kasuwa ba tare da an gano ba.
Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya ce jami’an NDLEA sun gano wannan sabon salo ne a yayin wasu ayyuka na musamman da suka gudanar kwanan nan a sassa daban-daban.
A cewarsa, waɗannan dabaru na nuna irin yadda masu fataucin ƙwayoyi ke ƙara zama masu dabara da rashin tausayi wajen kauce wa jami’an tsaro.
Babafemi ya yi gargaɗi ga ’yan ƙasa masu bin doka da oda da su kasance masu taka-tsantsan yayin tafiye-tafiye, tare da guje wa karɓar kaya ko jakunkuna daga hannun kowa.
NDLEA ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ƙarfafa matakan daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi domin kare lafiyar al’umma da tsaron ƙasa.