Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA sun kama wata mai shekaru 50 bisa zarginta da yunƙurin safarar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.3 ta hanyar amfani da ciki na karya.
An kama wacce ake zargin, Misis Ifeoma Ezewuike a tashar mota da ke unguwar Jibowu, a unguwar Yaba kan hanyarta na safarar hodar zuwa Abuja.
Bayan an kammala bincike za a gurfanar da ita a gaban kotu.