NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar BECE Na 2026
Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta sanar da fitar da sakamakon Jarabawar Kammala Makarantar Sakandaren Farko (BECE) ta shekarar 2026.
Mukaddashin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Azeez Sani, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
A cewarsa, ɗalibai 186,291 ne suka yi rajistar jarabawar a fannoni 12 daban-daban, inda suka fito daga jihohi 36 na Najeriya, Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma wasu ƙasashe biyar na waje.
Ya ce an fara gudanar da jarabawar ne a ranar 20 ga Afrilu, 2026, kuma aka kammala ta a ranar 30 ga Afrilu, 2026 cikin nasara.
Sani ya bayyana cewa an fitar da sakamakon ne bayan kammala taron Kwamitin Bayar da Sakamakon BECE na shekarar 2026 da aka gudanar a hedikwatar NECO da ke Minna, Jihar Neja.
A yayin taron, shugabar kwamitin kuma Daraktar Ilimin Farko ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folake Olatunji David, wadda ta wakilci Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ta nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da dukkan matakan da suka kai ga fitar da sakamakon.
Taron ya samu halartar shugabannin wasu makarantun sakandare daga sassan ƙasar da kuma manyan jami’an NECO.
Hukumar ta kuma amince da gudanar da jarabawar BECE Re-sit ga ɗaliban da suka samu gazawa a darasin Lissafi (Mathematics) ko Turanci (English Studies), ko kuma duka biyun.
Za a gudanar da jarabawar ne a ranakun 22 da 23 ga Yuli, 2026.
NECO ta ce an tanadi wannan jarabawa ne domin bai wa ɗaliban da abin ya shafa damar gyara sakamakonsu a darussan Lissafi da Turanci, ta yadda za su samu cancantar shiga aji na ɗaya na babbar sakandare (SSS1) ba tare da maimaita shekarar karatu gaba ɗaya ba.