NERC ta bai wa masu sola damar sayar da lantarki ga kamfanonin wuta

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da fara amfani da wani sabon tsari da zai bai wa masu samar da lantarki ta hanyar hasken rana (sola) damar sayar da ƙarin wutar da suke samarwa ga kamfanonin rarraba lantarki a ƙasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa, inda ta ce duk wanda tsarin sola ɗinsa ke samar da wutar lantarki fiye da buƙatarsa zai iya sayar da ragowar wutar ga kamfanin rarraba lantarki tare da samun kuɗin da ya dace.

A cewar NERC, sabon tsarin mai suna “Prosumer” zai bai wa mutum damar kasancewa mai amfani da lantarki kuma a lokaci guda ya zama mai samar da ita.

Sai dai hukumar ta ce akwai wasu sharuɗɗa da dole ne a cika kafin mutum ya amfana da tsarin. Daga cikin sharuɗɗan akwai kasancewa kwastoma a wani kamfanin rarraba lantarki da kuma mallakar tsarin sola mai ƙarfin akalla kilowatt 50 (50kWp).

Haka kuma, mai son shiga tsarin dole ne ya samu amincewar kamfanin rarraba lantarki da yake hulɗa da shi, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsarin, sannan ya yi rajista a hukumance da NERC.

Hukumar ta jaddada cewa sabon tsarin ba ya shafar yawancin gidajen da ke amfani da ƙananan tsarin sola na gida, domin an fi tsara shi ne ga manyan masu samar da lantarki da ke da ƙarfin samar da wuta fiye da bukatarsu.

NERC ta bayyana cewa tsarin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na bunƙasa amfani da makamashi mai sabuntawa da kuma ƙara yawan wutar lantarki da ake samu a ƙasar.

Comments (0)
Add Comment