Nijar ta katse hulɗa da Najeriya dau sauran wasu manyan kasashe

Kamar yadda BBCHausa suka wallafa, sun bayyana gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke hulɗa da Najeriya da Togo da Amurka da kuma wadda ta raine ta, Faransa bayan tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin da suka hamɓarar da shugaba Bazoum ta gaza samun matsaya da sojojin.

A wani jawabi da ya yi ta kafar yaɗa labaran ƙasar ta Nijar, jagoran juyin mulkin, Kanar Amadou Abdramane ne ya sanar da matakin da ma wasu matakan da suka ɗauka.

Ya ce “Mun kawo ƙarshen duk wata hulɗar jakadanci da Najeriya da Faransa da Togo da kuma Amurka. Duk wata matsaya da aka cimma a baya ta rushe.”

Tawagar da Ecowas ta tura don tattaunawa da sojojin Nijar ɗin a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar ta gana da wasu daga cikin sojojin a ranar Alhamis amma ba a cimma wata matsaya ba.

Manyan hafsoshin sojin ƙasashen Ecowas sun kammala wani taro a birnin Abuja, inda suka tattauna yiyuwar ɗaukar matakin soji a kan Nijar idan sasanci ya gagara.

Comments (0)
Add Comment