Nijar ta soke yarjejeniyar tattara bayanan sirri tsakaninta da Rasha da Turkiyya

Gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar tattara bayanan sirri tsakaninta da ƙasashen Rasha da Turkiyya.

Gwamnatin sojin ta ce ta yi hakan ne saboda rashin gamsuwa da irin ingancin fasahar na’urori da dabarun aikin da waɗannan ƙasashe suka ba ta, kamar yadda shafin intanet na LSI-Africa mai zaman kansa ya ruwaito.

Rahoton ya kuma ce wata sabuwar yarjejeniya tsakanin Nijar ɗin da wani kamfani na Maroko da ke da ƙwarewa a aikin tattara bayanan sirri ta hanyar latironi ta katse bayan da gano kamfanin na da alaƙa da wani kamfanin Faransa.

Nijar ta katse hulɗa da ƙasashen Yamma tare da ƙulla ƙawance da ƙasashen Rasha da Turkiyya ne tun bayan juyin mulkin da Janar Abdirahmane Tchiani ya jagoranta a watan Yulin 2024

Comments (0)
Add Comment