NUPENG Ta Kaurace Wa Taron Sulhu da Gwamnati Kan Yajin Aiki

Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas, NUPENG, ta gaza halartar taron sulhu da gwamnatin tarayya ta shirya kan shirin yajin aikin yan kwadago.

Ministan kwadago Muhammad Dingyadi ne ya gayyaci taron domin sasanta rikicin dake tsakanin NUPENG da kamfanin Dangote, bayan ƙungiyar ta dage cewa dole a baiwa ma’aikatanta damar shiga ƙungiya.

Gwamnati ta roƙi NUPENG da ta sake tunani kan yajin aikin da aka sanar, tare da bukatar NLC ta janye gargadin da ta baiwa ƙungiyoyin haɗin gwiwa su shirya shiga yajin neman adalci.

Sai dai rahotanni sun nuna har ya zuwa ƙarfe biyu da rabi na rana ranar yau Litinin, taron da aka tsara zai fara da ƙarfe goma na safe bai fara ba, abin da ya ƙara tsananta fargaba.

Comments (0)
Add Comment