NYSC ta sanya ranar 10 ga Yuni domin fara sansanin 2026 Batch B Stream I

Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya, National Youth Service Corps (NYSC), ta sanar da cewa za a fara atisayen sansanin horaswa na masu yi wa ƙasa hidima na rukuni na 2026 Batch B Stream I daga ranar Laraba 10 ga watan Yunin 2026.

Hukumar ta bayyana cewa za a fara karɓa da rajistar masu yi wa ƙasa hidima a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja daga ranar da aka tsara fara sansanin.

A cewar NYSC, za a rufe rajistar ne da tsakar daren ranar Juma’a 12 ga watan Yuni, ranar da kuma za a gudanar da bikin rantsar da sabbin masu bautar ƙasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa atisayen sansanin zai ci gaba har zuwa ranar Talata 30 ga watan Yunin 2026.

Hukumar ta yi wa dukkan masu yi wa ƙasa hidima fatan tafiya lafiya zuwa sansanoninsu da ke faɗin ƙasar nan, tare da sake jan hankalinsu kan haɗarin yin tafiya cikin dare.

NYSC ta shawarci masu yi wa ƙasa hidima da su daina tafiya da zarar ƙarfe 6:00 na yamma ya yi, tare da neman mafaka a wuraren da aka amince da su kamar masaukan NYSC, barikin sojoji, ofisoshin ’yan sanda ko fadodin sarakunan gargajiya kafin su ci gaba da tafiya washegari.

Hukumar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarinta na tabbatar da tsaron rayukan masu bautar ƙasa yayin zirga-zirga zuwa sansanonin horaswa.

Comments (0)
Add Comment