Obi Ya Nuna Shakku Kan Gaggauta Zartar da Dokar ‘Yan Sandan Jihohi

Obi Ya Nuna Shakku Kan Gaggauta Zartar Da Dokar ‘Yan Sandan Jihohi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya soki yadda Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gaggauta amincewa da kudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi (State Police), yana mai cewa an kauce wa ƙa’idojin majalisa, lamarin da ya haifar da shakku kan manufar siyasar da ke tattare da kudirin.

Obi ya kuma buƙaci a dakatar da aiwatar da dokar har sai bayan babban zaɓen shekarar 2027.

A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da karatu na biyu na kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ne ya gabatar da ƙudirin dakatar da wasu ƙa’idojin majalisar domin hanzarta duba kudirin da gwamnatin tarayya ta gabatar.

Da yake mayar da martani ta shafinsa na X, Obi ya ce duk da cewa buƙatar kafa ‘yan sandan jihohi ta daɗe tana samun goyon baya daga masana tsaro da masu ruwa da tsaki, hanyar da aka bi wajen zartar da kudirin ba ta gamsar ba.

Ya ce ya kamata a bai wa al’umma damar bayyana ra’ayoyinsu ta hanyar sauraron ra’ayin jama’a, musamman kan irin wannan muhimmin batu da ya shafi tsaron ƙasa.

A cewarsa, gaggauta zartar da kudirin ba tare da bin cikakkun matakan majalisa ba na ƙara haifar da zargin cewa akwai wata manufar siyasa a bayan sa.

Obi ya kuma bayyana fargabar cewa gwamnoni na iya amfani da rundunar ‘yan sandan jihohi wajen murƙushe abokan hamayyarsu na siyasa, tarwatsa gangamin jam’iyyun adawa da kuma yin tasiri a zaɓe.

Ya ce domin tabbatar da cewa rundunar za ta yi aiki ne domin jama’a, dole ne dokar ta tanadi wata hukuma mai zaman kanta a matakin jiha da za ta riƙa sa ido kan ayyukan rundunar ba tare da tasirin gwamnati ba.

Obi ya ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu, babu tabbacin cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi amfani da tsarin ‘yan sandan jihohi wajen yin tasiri a babban zaɓen 2027 ba.

Saboda haka, ya buƙaci a jinkirta fara aiwatar da dokar har sai bayan kammala zaɓen 2027 domin kauce wa duk wani zargi ko rashin amincewar jama’a.

Comments (0)
Add Comment