Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke na tabbatar da cancantar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya kawar da duk wata tangarɗa da ke gabansa.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin riƙo na ƙasa na PDP, Ini Ememobong ya fitar, inda ya ce hukuncin kotun ya yi daidai da doka da kuma hankali.
PDP ta ce wannan hukunci, haɗe da sassaucin sharudan tantancewa da jam’iyyar ta bai wa Jonathan, ya share masa fagen shiga takarar shugaban ƙasa kafin zaɓen fidda gwani da za a gudanar nan gaba kaɗan.
Jam’iyyar ta kuma bayyana ƙarar da wani lauya daga Abuja, Johnmary Jideobi ya shigar a matsayin bata lokaci da amfani da kotu ta hanyar da ba ta dace ba.
Tun farko dai mai ƙarar ya nemi kotu ta hana Jonathan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa, yana mai hujjar cewa tsohon shugaban ya riga ya sha rantsuwar kama aiki sau biyu a matsayin shugaban ƙasa.
Sai dai kotun ta bayyana cewa sashe na kundin tsarin mulki da aka jingina ƙarar a kansa ba zai iya aiki kan abin da ya faru kafin samar da dokar ba.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa Jonathan na da cikakkiyar damar sake neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.
PDP ta ce hukuncin ya ƙara tabbatar da cewa dokoki ba sa aiki kan abubuwan da suka gabata, tare da yabawa kotun kan tara da ta ci mai ƙarar domin hana amfani da shari’a wajen kawo cikas ga dimokuraɗiyya.
Duk da cewa Jonathan bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, wasu manyan jiga-jigan PDP na ci gaba da matsa masa lamba domin ya dawo takarar shugaban ƙasa a 2027, yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin sake farfaɗowa bayan shan kaye a zaɓukan baya.