PDP ta Nemi Gwamnati da Ta Yi Bayanin Yadda aka Kubutar da ‘Yan Coci 38 a Kwara

Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta yi kira ga gwamnati ta fito fili ta bayyana hakikanin yadda aka kubutar da mutane 38 da aka sace daga cocin Christ Apostolic Church, da ke Eruku.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Olusegun Olusola Adewara, ya fitar, jam’iyyar ta ce akwai tambayoyi da dama da jama’a ke yi game da yadda aka ceto mutanen—tambayoyi da gwamnati ke da alhakin amsa su.

PDP ta nemi sanin: Shin an kama waɗanda suka kai harin? Ko an biya kuɗin fansa kafin a sako mutanen? Wadanne tsare-tsare gwamnati ta yi don tallafawa waɗanda abin ya rutsa da su? Kuma me gwamnati ke shirin yi domin kaucewa irin wannan ta’addanci a nan gaba?

Jam’iyyar ta ce jama’a na bukatar cikakken bayani, ba takaitaccen jawabi ba, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya zama dole, ba zabin gwamnati ba.

Comments (0)
Add Comment